DOKOKI A HUKUMANCE NA HALARTA DA KARƁAR LADA

1. HALARTA DA DOKOKIN LADA

Waɗannan dokoki na halarta da lada (“Dokoki”) sun shimfiɗa damammaki da nauyaye-nauyaye na mai halarta da kuma ƙa’idoji na yadda za a karɓi lada saboda kasancewa wani ɓangare na dandali wanda Human8 ta shirya a kan kowane daga cikin dandamalinsu. Ana shirya waɗannan dandamali a matsayin wani ɓangare na aikace-aikacen bincike a kan kasuwanci wanda Human8 take yi a madadin abokan cinikinta (“Abokan ciniki”). Saboda haka, ta hanyar halartarka a cikin dandalin da kuma amfani da dandamalinmu, ana buƙatar mai halartar ya:

 •  karanta kuma ya yarda da Dokokin;
 • ya tabbatar da bin tanade-tanade na waɗannan Dokoki kuma ya yarda cewa idan aka sami karya Dokokin, za a soke halartar su a kowane dandali kuma ko Ladan zai kasance lalatacce.

Human8 na iya gyara waɗannan Dokoki a kowane lokaci kuma ta sanar ta hanyar ɗabba’a bugun da aka sabunta na Dokokin a dandamalin a ƙarƙashin sashin manufar lada dake saɗarar ƙasa. Dokokin wani tsari ne baki ɗaya kuma za a iya keɓance su kuma a yi bayaninsu (ya danganta da dandalin da kuma aikin) a kan katin ladan da kuma FAQ.

A halin wani hilafa ko mara dacewa tsakanin sharuɗɗa da kuma ƙa’idoji na waɗannan Dokokin Hukuma da kuma bayyanawa ko sauran jimloli da suke cikin wasu kayayyaki dangane da kyaututtuka, da suka haɗa, amma ba su taƙaita ga: fom na shigarwa, wurin gizo, waɗannan Dokokin Hukuma, ko talla, sharuɗɗan da kuma ƙa’idoji na waɗannan Dokokin Hukuma za su rinjaya, gudana da kuma sarrafa har cikakkiyar iyaka da ake yarda ta wajen doka.

2. TSARAWA

Kamfen ɗin Human8 na kamfani ne mai taƙaitaccen iko wanda ke da rajista a ƙarƙashin dokar Belgium mai lamba 0837.297.070, mai lambar wurin zama a Evergemsesteenweg 195, 9032 Wondelgem, wanda a nan gaba za a ci gaba da kira “Human8 ”.

Human8 tana aiki kuma tana gudanar da dandali (Al’ummu masu hange na kan yanar-gizo wani dandamali ne na kan yanar-gizo wanda ke haɗa al’umma domin halartar aikace-aikace na nazarin nau’ika. Tana samun dubawa daga wani haziƙin mai kula kuma zai iya samun mabanbantan lokuta daga gajere zuwa wanda zai ci gaba.) a kan dandamalinta na Square a madadin Abokan cinikinta. Zai iya faruwa cewa wasu al’ummun suna samun gudanarwa daga Abokan cinikinta da kan su a kan dandamalin InSite. A cikin waɗannan al’ummu za a gayyaci masu halarta kuma za su shiga cikin wasu aikace-aikace daban-daban, da suka da amma basu taƙaita ga:

 • Aikace-aikacen gwajin ra’ayi;
 • Gwajin kayayyaki;
 • Dandalin tattaunawa;
 • Nazari;

(“Aikace-aikacen” ko “Aiki”)

Kowane aiki yana da jerin ƙa’idojinsa domin samun cancantar halarta. Saboda haka, ba kowaɗanne mahalarta ne za su cancanta domin samun wani Aikin ba, kawai masu halarta da suka cika ƙa’ida ne za a gayyata. Wannan ya ƙunshi cewa idan kana cikin wani Dandali, ba za ka sami gayyata zuwa dukkan Aikace-aikace da aka ƙaddamar a wannan Dandalin ba.

3. HALARTA

3.1 Cancanta

Domin cancantar kasancewa ɓangare na kowace al’umma ana neman masu halarta cewa:

 • suna da iyawa a dokance kuma sun yarda su yi biyayya ga waɗannan Dokoki;
 • ba sa ƙasa da shekaru 18, idan ba haka ba iyayensu/masu kula da su bisa doka sun yarda a bayyane da waɗannan Dokoki;
 • ba su sami aiki da kowane sashe na rukunin Human8 ba a duk faɗin duniya;
 • ba su da dangantaka ta jini ko aure ga wani ma’aikaci na kowane sashe na rukunin Human8 a duk faɗin duniya;
 • su ba wani ɓangare ne na iyalin wani ma’aikaci na kowane shashe a rukunin Human8 a duk faɗin duniya ba.

3.2 Kora

Idan Human8 ta yi zargi, kamar yadda ta ga ya dace, ko kuma abokin cinikinta ya sanar da ita cewa wani mai halarta:

 • ya shiga cikin kowane irin aiki na yaudara ko haramtacce (wanda ya haɗa amma bai taƙaita ga ƙirƙirar furofayil daban-daban na bayar da amsa domin shiga fiye da ɗaya cikin wani aiki, yin rashin gaskiya dangane da furofayil nasu);
 • bai yi aiki dangane da tanadin dokoki a hukumance ba da/ko
 • yana nuna ‘mummunan’ hali na mai halarta (mummunan hali ya haɗa da amma bai taƙaita ga gaggawa (wato idan lokacin da aka kashe na kammala wani aiki ko nazari bai kai kaso 50 daga cikin ɗari na matsakaicin lokaci ba, wanda ke nuna cewa tambayoyin/ aikace-aikacen ba a amsa su daidai ba), zaɓar amsa iri guda (wato zaɓar amsa iri guda domin jerin tambayoyi daban-daban a cikin wani nazari) ko kuma samar da amsoshin da ba daidai ba ko bayanan da ba cikakku ba (wato daɗa maimaita ko amsoshi masu gaɓa guda ga yawaici ko dukkan tambayoyi/ aikace-aikace)), ko bayar da amsa tare da ƙarancin ƙoƙari a cikin tattaunawa da kuma ƙalubalen al’umma.

(baki ɗaya da ake kira “Halayyar Kora”)

Human8 ko Abokan cinikinta, a duk lokacin da suka ga ya dace, na da dama ta korar wannan mai halarta, saryar da makunkuna na mai halarta, riƙe samun dama ko samo abubuwan ƙarfafa gwiwa ko Lada (a kowane nau’i duk yadda yake) kuma/da cire mai halarta daga Aikace-aikacen, al’umma, nazarin bincike da/ko ƙungiyoyi. Zuwa iyakar gwargwadon da doka ta bari, babu yadda za a yi Human8 ta ɗauki alhaki na kowace irin asara, lahani (kai tsaye ko ba kai tsaye ba) wadda Mai halarta ya haɗu da ita sakamakon korar ko kuma kowane irin mataki da Human8 ta ɗauka a dalilin Halayyar Kora ta Mai halarta.

Idan Human8 ko kuma kowane daga cikin Abokan cinikinta ya sami kowane irin lahani (kai tsaye ko ba kai tsaye ba) sakamakon Halayyar Kora daga mai halarta, mai halarta zai tabbatar da cewa Human8 da/ko Abokan cinikinta ba su da cutarwa daga lahanin da aka samu.

4. HANYAR SAMUN MAKUNA DA KUMA LADA DAGA BAYA

4.1 Tattara makuna

Za a samu wani lada bisa dogara da makunan da wani mai halarta ya samu. Za a iya musayar makuna domin Ladaddaki. Kowane Aiki yana da Ladaddaki nasa da kuma makuna. Za a iya samun makuna ta hanyar kammala wani aiki ko jerin aikace-aikace ta hanyar kiyayewa da wani daidaitaccen tsari (ma’ana ingancin kammalawa/amsoshi) dangane da Dokoki da suka dace a cikin wani tsarin lokaci. Makunan da aka samu za a ƙara su ta otomatik a cikin abin da ya yi ragowa na mai halarta a ƙarƙashin Shafin Ladaddaki Nawa da zarar aikin ya rufe.

Za a iya samun cikakken bayanin kowane Aiki a cikin aikin da kuma a kan katin aikin. Za a yi bayanin yadda za a sami makuna a kan katin lada da kuma a cikin sashin FAQ. Wannan bayanin aƙalla zai haɗa da (I) adadin makuna da za a iya samu ta hanyar kammala Aikin (ii) fayyataccen lokaci (wanda ya haɗa da kwanan watan farawa).

Domin kawar da shakku, masu halarta za su iya samun makuna ta hanyar kammala Aikace-aikace a ƙarƙashin sharaɗin cewa ingancin amsoshinsu/kammlawa ya cim ma ingancin da Human8 ko Abokan cinikinta suka tsara. Human8 ko Abokan hulɗarta ne za su tabbatar da ingancin amsoshin, kamar yadda suka ga ya dace. Za a ɗauki amsa a matsayin isasshiya idan wannan amsar tana bin tsarin da aka bayar a cikin aikin yadda ya kamata. Idan amsar ta gaza cim ma ingancin da Human8 ko Abokan cinikinta suka tsara sannan a sakamakon haka ba a ɗauke su a matsayin ingantacciyar amsa ba, Human8 ko Abokan cinikinta za su sami dama ta cire, ƙin amincewa da amsar sannan kuma babu wasu makuna da za a bayar.

Koyaushe makuna cikakkun lambobi ne daga 1 zuwa sama. Koyaushe Human8 ko abokan cinikinta ne ke da damar shigarwa da hannu a kan Shafin Ladaddaki Nawa sannan su canza makunan da aka samu idan (ya haɗa amma bai taƙaita ga) (i) mai halarta ya gudanar da Mummunar Halayya (ii) aka lura cewa masu halarta ba sa aiki (duba sashi na ƙasa) (iii) Ya zama wajibi Human8 ta shiga domin bayar da Ladaddaki da hannu.

4.2 Ƙarewar ladaddaki

Har lokacin da mai halarta yake cikin aiki a kan Dandalin kuma yana shiga cikin Ayyuka da aka gayyaci mai halarta zuwa gare shi, Makunan da aka samu suna da inganci. Aiki ya haɗa da samar da ingantattun amsoshi da kuma kammala Ayyuka.

Har sai idan tuni an bayyana saɓanin haka, za a iya zaton cewa masu halarta ba sa aiki idan suka gaza samar da ingantacciyar amsa na aƙalla Aikace-aikace guda 6 a jere a inda aka gayyace su zuwa gare shi a cikin tsawon kwanaki 365. Kawai a halin da mai halarta bai ba da amsa ga gayyace-gayyace guda 6 a jere daga waɗanda aka aika aƙalla guda 1 a cikin rabi na farko kuma aka aika aƙalla 1 a cikin rabi na biyu na kwanaki 365, makunan za su ƙare aiki. Mai ƙirga na Shafin Ladaddaki Nawa zai nuna adadi na makuna 0.

Idan mai halarta ba ya aiki, makunan za su daina aiki daga lokacin da ya/ta gaza bayar da amsa a kan lokaci (manufa, ya kamata amsar ta afku kafin kwanan watan ƙarewar aikin) kuma cikin inganci zuwa gayyata ta 6.

Bayan an rufe Dandalin, sauran makunan da mai halarta ya samu lokacin gudanar da aiki za a rasa su. Shafin ladan zai nuna cewa lambar makunan zai kasance 0. A halin da aka sake buɗe Dandalin, ba za a sami makunan ba kuma.

4.3 Ladaddaki

Ya danganta da adadin makunan da kowane mai halarta ya samu za a iya bayar da Lada. A wasu lokutan, wannan na iya faruwa ta otomatik (ta hanyar samun wani gwargwado ko kuma daga taimakon Human8 ko Abokin cinikinta) ko kuma mai halartar shi kan sa zai iya zaɓar nemo makunansa domin Lada. A wannan halin, masu halarta na iya danna madannin nema domin karɓar Ladansu. Za a ba ka Ladanka cikin gwargwadon lokacin da ya dace, za a iya samun ƙarin bayani a kan katin lada ko FAQ. Za ka sami imel kuma za a nemi ka ba mu dukkan bayanan da suka zama wajibi na ƙashin kan ka domin ba ka ladaddakin (waɗanda suka kasance cikakken suna da adireshi). Wannan mahaɗi na tabbatarwa na bayani na ƙashin kai zai kasance mai inganci na tsawon kwanaki 90, wanda bayan wannan lokaci ladan zai lalace kuma har abada ba za ka sake san damar nemo shi ba.

Ya danganta da Dandalin da kuma abokin hulɗa na ladan (da kuma samuwar ladan) Ladan na iya kasancewa ɗaya daga cikin waɗannan kayayyaki:

 • Bauca;
 • Kaya;
 • Zaɓin biya ta yanar-gizo;

(“Ladan”)

Baucoci sun rataya ne ga sharuɗɗa da ƙa’idojinsu. Masu halarta ba su cancanci ƙima ta kuɗi ba. Baucoci na iya fayyace lokaci wanda ya zama wajibi a karɓe su. Human8 ko Abokin cinikinta ba su ke da nauyi ba idan bauca ta ɓata, sacewa, ko ta daina aiki ko aka lalata ta kuma ba za a bayar da musayarta ba a waɗannan yanayi. Ba su da inganci a kan saye-saye na gabanni. Ba za a maye gurbin kyaututtuka ba idan an yar da su ko an sace su. Babu halin da zai sa darajar Ladan da aka karɓo ya wuce darajar baucar da aka bayyana.

Abokan ciniki ko wani daban wanda suka zaɓa na iya bayar da kayayyakin. Babu halin da za a ɗorawa Human8 nauyi na rauni ko rashin yin aiki na wani kaya da ko lahani da za a iya samu daga mai halarta a sakamakon waɗannan rauni ko rashin yin aiki.

Human8 ko Abokan cinikinta ba za su taɓa ɗaukar nauyi na kowane irin cajin kuɗi ko musayar canjin kuɗi dake da alaƙa da kowane Lada. Masu halarta sun yarda cewa nau’in Ladan ya danganta da samuwar ladan kuma yana da alaƙa da abokin hulɗa na ladan da kuma wurin zama na wannan abokin hulɗa na ladan. Ba za a ɗorawa Human8 alhaki ba idan Ladan ya daina samuwa.

Ana buƙatar masu halarta su yi biyayya ga dukkan dokoki da ƙa’idoji da suka dace domin karɓar waɗannan Ladaddaki (wanda ya haɗa amma bai taƙaita ga ƙa’idojin haraji na kuɗin shiga ba).

5. BAYANI NA ƘASHIN KAI

Human8 za ta sarrafa bayani na ƙashin kai da masu halarta suka bayar bisa dacewa da manufar sirrinsa. Ta shigarwa dandalin, kowane mai shigarwa yana yarda dalla-dalla ga Human8 , ajan ɗinsa da kima ko wakilan su ajiye, raba, da kuma yi amfani da keɓaɓɓen bayani da aka miƙa tare da shigarwa, bayanin rajista da kuma amsoshin aiki gwargwadon Dokar Tsare Sirri ɗin.

6. WARANTI DA DIYYA

Dukkan masu halarta za su cire diyya da kuma riƙe Human8 da Abokan cinikinta daga rashin cutarwa daga kowane damu, mataki, iƙirari, nema, adawa, nauyi, rasawa, lahani, farashi ko kashe kuɗi da aka samu ko fuskanta daga Abokan ciniki da/ko Human8 sakamako daga kowace irin saɓawa na waɗannan Dokoki ko amfani na dandalin.

7. BAYANIN KUƁUTA DA TAƘAITAR ƊAUKAR NAUYI

Babu yadda za a yi Human8 ta ɗaukin nauyi na: (i) kowane kasawa ta wurin gizo a lokacin wani aiki; (ii) kowane rashin aiki na fasaha ko wasu matsaloli dangane da hanyar sadarwa ko layuyyukan tarho, tsare-tsaren kan layi na kwamfuta, uwannin garke, masu samar da dama, na’urar kwamfuta ko sofwaya; (iii) kasawar wata shigarwa ko wani bayani da za a samu, ɗauka ko naɗa don kowane dalili, da suka haɗa, amma ba su taƙaita ga, matsalolin fasaha ko cunkoson tarafik a kan Intanet ko a wani wurin gizo ba; (iv) kowane rauni ko ɓarna ga wani mai shigarwa ko kwamfuta ko sauran na’ura ta kwamfuta ta wani mutum dabam dangane da ko sanadi daga halartawa cikin wani aiki; da kuma/ko (v) wani haɗewa na saman. Kowane rasit na kwamfuta na otomatik (kamar saƙon ‘mun gode’ ko tabbacin isarwar shigarwa ɗaya) ba su ƙunshi hujjar ainihin rasit ta Human8 na wata kammalawar aiki ba don dalilolin waɗannan Dokokin Hukuma.

Zuwa gwargwadon abin da doka ta bari, Human8 ba za ta ɗauki nauyi na kowace matsala ba, ƙorafi, adawa, iƙirari, ko lahani (i) dake da dangantaka da amfani na amsoshin da aka miƙa daga masu halarta (ii) dake da dangantaka da kowace saɓawa da waɗannan dokoki.

8. DOKAR DA TA DACE DA IYAKAR DOKA

Har sai idan an samar a ƙarƙashin dokokin da suka dace ko ƙa’idoji na yanayin manufa ta jama’a, waɗannan dokoki sun rataya ne ga dokar Belgium da kuma kowace ƙara ko saɓani da ka iya tasowa daga baya za a iya gabatar da su a gaban kotu yayin da aka sami iyakar doka a kan irin waɗannan matsaloli a Ghent.